Hukumar shige da fice a Najeriya NIS ta sanar da cewar wasu ƴan bindiga na shirin kai wasu hare-hare babban birnin tarayya Abuja.

Ƴan bindigan na shirin kai hare-haren ne a watan Disamban da mu ke ciki.

A wata sanarwa da shugaban hukumar Idris Jere ya fitar a yau, ya ce  maharan da za su kai hari na ƙasashen ƙetare ne.

Hukumar ta ce ta samu bayanan hakan ne ta ƙarƙashin ƙasa.

Maharan da ake zargi za su kai harin za su fito ne daga ƙasashen Mali, da Nijar sai kuma wasu da su ke cikin Najeriya.

Hukumar ta ce mutane su kwantar da hankalin su domin su na iya ƙoƙarinsu don ganin hakan ba ta kasance ba.

Leave a Reply

%d bloggers like this: