Gwamnatin tarayyar Najeriya ta sanar da bayar da garaɓasa ga ƴan ƙasar don yin tafiye-tafiye a jirgin ƙasa kyauta albarkacin kirsimeti.

Jami’in hulɗa da jama’a na hukumar kula da jiragen ƙasan Najeriya Mahmood Yakub ne ya sanar da haka a wata sanarwa da ya fitar.

Ya ce ƴan ƙasar za su kwashi albarkacin ranar kirsimeti na yi tafiye-tafiye kyauta tun daga ranar Juma’a 24 ga watan Disamba zuwa ranar 4 ga watan Janairun 2022.

Ya ce garaɓasar ta ƙunshi dukkanin jiragen da ke ƙarƙashin hukumar su ta Nigerian Railway Cooperation wato (NRC).

Wannan wani mataki ne da hukumar ta ɗauka hadin gwiwa da ma’aikatar sufuri ta Najeriya domin saukaƙa wa masu tafiye-tafiye a yayin bukukuwan sabuwar shekara da Kirsimeti.

Wasu daga cikin jihohin da za su iya kwasar garaɓasar akwai Legas, Abia, Rivers, Kano, Neja, Ibadan Kaduna da kuma babban birnin tarayya Abuja.

Leave a Reply

%d bloggers like this: