Wata ƙungiya mai rajin bibiya a kan yadda malaman sakandire a Kano ke gudanar da harkokin koyarwar su ta zaɓi gwarzon ta na shekarar 2021.

Ƙungiyar Stem Teachers Reward And Empowerment Foundation (STREF) ta zaɓi Malam Haruna Ali Isah wanda ya ke koyarwa a makaranatar sakandiren mata ta GGSS Ƙaraye a matsayin gwarzon shekarar 2021.

An zaɓi Injiya Haruna Ali Isa tare da ba shi lambar yabo ta girmama  wa duba ga yadda ya ke jajircewa wajen koyar da ɗalibai tare da tabbatar da sun fahimci darasin da ya ke koya musu.

Shugaban ƙungiyar Love Odion ta ce sun zaɓi gwarzon ne bayan bibiyar aikin koyarwar da ya ke yi har su ka aminta da jajircewar sa domin ciyar da ilimi gaba.

Haruna Isa wanda shi ne shugaban ƙungiyar Alƙaryata Rimin Kebe a ƙaramar hukumar Ungogo da ke Kano, ya nuna jin daɗin sa a bisa yadda ƙungiyar ta zaɓo shi tare da ba shi wannan lambar yabo.

Injiniya Haruna Ali ya zamto na farko da ƙungiyar ta karrama sai wasu sauran malamai huɗu da ke sauran makarantun sakandire daban-daban a Kano.

Babban sakatare a hukumar kula da makarantun kimiyya na jihar Kano Tijjani Ahmad Abdullahi ya taya gwarzon murna tare da jan hankalin sauran malamai da su yi koyi da irin yadda ya ke jajircewa tare da aiki tuƙuru domin ci gaban ilimi a jihar Kano.

 

 

Leave a Reply

%d bloggers like this: