Ya ce gwamnatin za ta yi amfani da fasahar zamani wajen ƙirƙirar aikin yi a tsakanin al’umma.

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya ce gwamnatin sa ba za ta ci gaba da zuba id ana ci gaba da kashe mutane a Najeriya ba.

A saƙn sabuwar shekara da shugaban ya aike wa ƴan Najeriya, Muhammadu Buhari ya ce a sabuwar shekarar 2022 da aka shiga gwamnatinsa za ta himmatu wajen ganin ta kawo ƙarshen kashe-kashen da ake fama da su a kasar.

Ya ƙara da cewa a halin yanzu da yawa daga cikin ƴan bindiga sun mika kan su ga jami’an tsaro.

Shugaban ya ce ana ci gaba da tsare-tsare dn ganin an ci gaba da samun mutanen da su ke miƙa wuya a wurare daban-daban.

Ya ce rashin tsaron da ake fama da shi a  ƙasar na iya sa ƴan ƙasar su gaza gano irin ɗumbin nasarorin da gwamnatin sa ta samar.

A cikin saƙon sabuwar shekarar  shugaba Buhari ya ce gwamnatin sa za ta yi duk mai yuwuwa wajen ganin ta yi amfani da fasahar zamani domin samar da aikin yi ga ƴan ƙasar.

Shugaban ya ce ƴan ƙasar su sa rai da samun ayyukan yi a sabuwar shekarar da mu ka shiga a yanzu.

Haka kuma ya jinjina wa ƴan Najeriya a bisa irin haƙuri da juriyar da su ka yi na ƙalubalen tsaro da ake ci gaba da fuskanta a ƙasar.

Leave a Reply

%d bloggers like this: