Rundunar ƴan sandan jihar Nassarawa ta tabbatar da kama wani mutum da ake zargi ya hallaka matarsa bayan samun saɓani da su ka yi.

Jami’in hulɗa da jama’a na rundunar ASP Ramhan Nansel ne ya tabbatar da haka a Lafiya babban birnin jihar.

Ya ce ana zargin mutumin ya hallaka matar tasa ne bayan sun samu sabani lamarin da ya kai ga ya fara dukanta har ta rasa ran ta.

Al’amarin ya faru a yammacin Juma’a a yankin Sabon Fegi-Shabu a Lafiya ta jihar Nassarawa.

Ƴan sanda sun kama Yakubu Ovye bayan samun rahoton zargin hallaka matarsa.

Tuni aka mika korafin zuwa sashen binciken manyan laifuka da kisan kai domin faɗada bincike a kai.

Sa’annan an aike da gawar matar zuwa wajen ajiyar gawarwaki kafin fara gudanar da bincike domin gano sanadiyyar mutuwarta.

Leave a Reply

%d bloggers like this: