Gwamnan jihar Yobe Maimala Buni ya ɗage takunkumin hana hawa babur mai ƙafa biyu a jihar.

Gwamna Maimala Buni ya bayyana haka ne a fadar sarkin Nguru yayin da ya je ziyarar jaje a bisa iftila’in gobara da ta tashi.
Bayan shafe kusan shekaru goma da hana hawa babur a jihar wanda aka haramta hawa tun a shekarar 2012 sanadiyyar hare-haren mayaƙan Boko Haram.

Gwamnan ya ce a halin da ake ciki yan jihar na da damar hawa babur ta yadda za su samu sauƙin zuwa gonakinsu da sauran wurare.

Ya ce makatin hakan ya zo ne bayan ci gaban da aka samu daga ɓangaren tsaro a jihar wanda ya ba su damar sassauta dokokin da aka saka yayin da aka matsa da rikicin mayaƙan Boko Haram.
An ɗage takunkumin a ƙananan hukumomi goma da ke ƙarƙashin yankunan kudu a arewacin jihar.
Ƙananan hukumomin sun haɗa da Potiskum, Nguru, Fika, Yusufari, Jakusko, Nangere, Karasuwa, Bade,Machina, da ƙaramar hukumar Fune.