Gwamnatin tarayya a Najeriya ta tsayar da watan Mayu domin fara ƙidayar yan ƙasar baki ɗaya.

Shugaban hukumar kidaya ta kasa National Population Comission ya ce a karon farko a shekaru 15 za a yi kidayar yan kasa a fadin Najeriya.

Shugaban hukumar Nasir Isa Kwarra ya ce za a yi amfani da fasahar zamani don ganin cewa an gudanar da ingantacciyar ƙidaya kuma karɓaɓɓiyar.

Karon farko ke nan da gwamnatin ta shirya yin ƙidayar ƴan ƙasar tun bayan shekaru sama da 15 wanda aka yi a shekarar 2006.

Wasu daga cikin kungiyoyin kudancin Najeriya ba su yarda da sakamakon kidayar da a ka gudanar ba a shekarar 2006, su na zargin an yi magudi domin fifita yankin arewacin najeriya.

Kiyasi ya nuna cewa al’ummar Najeriya sun kai miliyan 200 idan aka kamanta da miliyan 140 da aka samu a 2006.

Sai dai har yanzu ana jiran shugaba Muhammadu Buhari ya amince da ranar da za a gudanar da kidayar.

Leave a Reply

%d bloggers like this: