Gwamnatin jihar Kano ta soke lasisin dukkanin makaratu masu zaman kansu na faɗin jihar Kano.

Kwamishinan ilimi a jihar Kano Sanusi Sa’id ƙiru ne ya sanar da haka a yayin gana wa da manema labarai yau Litinin.
Ya ce an soke lasisin dukkanin makarantu masu zaman kansu har sai an tantance su tare da basu takardar shaida.

Matakin da aka ɗauka an sanya hukumomin tsaro na DSS hukumar kare fararen hula da sauran jami’an tsaro domin tabbatar da sake bin diddigin lasisin makarantun.

Hakan ya biyo bayan samun rahoton kisan wata ɗaliba mai shekaru biyar a duniya wadda ake zargi malamin makarantar bokon su ya hallaka ta ta hanyar ba ta maganin ɓera.
Malamin ya yi garkuwa da ɗalibar ta sa ne sannan ya buƙaci kudin fansa naira miliyan shida.
Jami’an tsaro sun kama wanda ake zargin kuma tuni ya amsa laifinsa.
Wasu fusatattun matasa sun ƙone makarantar da ke unguwar Tudun Murtala a ranar Lahadi wayewar Litinin.