Jami’an tsaron hadin gwiwa a jihar Neja sun samu nasarar kashe ƴan bindiga da dama a jihar tare da kɓutar da shanu 300.

Jami’an tsaron sun kashe ƴan bindigan ne a wasu ƙauyuka da ke ƙananan hukumomin Shiroro da Munya.
Baya ga shanu 300 akwai sauran dabbobi da aka kuɓutar uda 200.

Kwamishinan tsaro a jihar Emmanuel Umar ya tabbatar da faruwar lamarin, ya ce biyar daga cikin shanun sun mutu kafi a kai su Minna babban birnin jihar.

A yayin artabun da aka yi da jami’an staro akwai wasu daga ciki da su ka rasa rayukansu.
Ya ƙara da cewa za a bai wa iyalansu kulawar da ta dace.