Rundunar yan sandan jihar Yobe ta ce ta kama wasu mutane uku da suka hada da soja guda da laifin hada baki da fasa gidaje da kuma fashi da makami.

Waɗada ake zargin sun kai farmaki gidan wata Hajiya Aisha Usman da ke unguwar Sabon-pegi a Damaturu da tsakar dare.

Mutane uku da ake zargin dauke da muggan makamai da suka hada da bindiga kirar AK47 sun yi awon gaba da kudi naira 250,000 da mota kirar Peugeot Saloon 307 da kuma wayar salula mallakin wanda aka kashe.

A wata sanarwa da jami’in hulda da jama’a na rundunar yan sandan jihar Yobe ASP Dungus Abdulkarim ya fitar a yau Asabar ya ce wadanda ake zargin sun yi wa matar da danta Ahmed Umar mai shekaru 17 raunuka masu tsanani bayan daure su da waya.

ASP Dungus ya bayyana cewa an kama biyu daga ciki yan fashin ne a garin Damaturu na ukun su kuma wanda motar take hannunsa an kamashi ne a garin Darazo na jihar Bauchi.

Ya ƙara da cewa sojan da aka kama ya na aiki ne da runduna ta 12 karkashin rundunar Operation Hadin kai da ke aiki a Damaturu sauran kuma matasa ne da ke zaune a garin.

Yanzu haka sojan da abokan fashin nasa  suna fuskantar zargin shiga gida ba da izini ba aikata fashi da makami da sauran laifukan ta’addanci.

Leave a Reply

%d bloggers like this: