Jam’iyyar PDP reshen jihar Kano ta buaci hukumar hana cin hanci da rashawa EFCC ta su dakatar da gwamnan Kano a kan yunurin barbaɗar da kuɗin al’ummar jihar

Shugaban jam’iyyar Shehu Wada Sagagi ne ya sanar da haka a wata takarda da ya sanya wa hannu.
Jamiyyar ta nuna takaicinta a kan yadda majalisar zartarwa ta jihar ta amince da fitar da kudin da ya haura naira miliyan 500 domin gyaran gadar ƙasa a Ƙofar Ruwa.

Sanarwar ta ayyana aikin da gwamnatin ta ɗauki aniyar yi a matsayin almubazzaranci ga dukiyar jama’a

Jam’iyyar ta buƙaci hukumar EFCC ta da takatar da gwamnan daga yunƙurin ƙawata gadar da su ka ɗauki aniyar yi.
Sa’annan sun buƙaci ƙungiyoyin al’umma da jama’ar Kano da su yi watsi da aikin ganin cewar akwai buƙatu da dama waɗanda su ka shafi al’umma.