Kwamishinan al’amuran tsaro a Kaduna Samule Aruwan ne ya bayyana hakan yayin da ya ke gabatar da rahoto a kan tsaro a Kaduna.

Samuel Aruwan ya ce an hallaka mutane 1,192 yayin da ƴan bindiga su ka yi garkuwa da mutane 3,348 a jihar Kaduna.
Ya ƙara da cewa daga cikin mutane 1,192 da aka kashe akwai maza 1,038 yayin da aka kashe mata 104, sai yara 50.

A tsakiyar birnin Kaduna an hallaka mutane 720 sai kudancin jihar aka kashe mutane 406.

Rahoton shekarar wanda kwamishinan ya gabatr wa gwamnan jihar Malam Nasir El’rufa’i a yau Talata, ya ce dukkanin bayanan sun tatara ne a kan kisan gillar da ƴan bindia su ka yi wa jama’ar a shekarar 2021.