Huukumar lafiya ta duniya WHO ta ce annobar cuutar Korona na raguwa a nahiyar Afrika.

Hukumar ta ce an samu raguwar yaduwar nau’in cutar a kudanci da yankin sahara a makonni biyu da su ka gaba.
Sai dai wasu kasashe kamar Tnusia da Moroko da kasar Aljeriya na fuskantar yaduwar cutar.

Alkalman da hukumar ta tattara ta ce cutar ta ragu da kaso 40 cikin 100 a nahiyar Afrika.

A tsakiyar Afrika an samuu ragwar cuutar da kaso 68 cikin 100 yayin da cutar ta ragu da kaso 60 cikin 100 a yammacin Afrika sai kuma gabashin Afrika da aka samu raguwar cutar da kaso 47 cikin 100.
Cutar Korona ta haifar da cikas a kan udanarwar al’amura a fadin duniya musamman yankin kasashen turai.