Majalisar dokoki a Najeriya ta buƙaci jami’an tsaro su ɗauki mataki a kan kashe-kashen da ake yawan yi a ƴan kwanakin nan.

A zaman majalisar na yau Laraba, majalisar ta ce an samu karuwar kashe-kashen al’umma a Najeriya a kwanakin nan.
Wani ɗan majalisa daga jihar Enugu ne ya gabatar da takardar a gaban majalisar, wanda ya ce hatta sace-sacen jama’a ma ya ƙaru a Najeriya.

Ya ce a watan Janairun da ya gabata, sai da aka samu rahoton kisan wasu mutane a jihar Ogun.

Ya ƙara da cewa yawan al’ummar da aka kashe a Najeriya sun kai 10,480 kamar yadda hukumar bayar da agajin gaggawa ta Red Cross ta bayyana.
Majalisar ta bukaci jami’an tsaro su ɗauki matakin gaggawa domin magance matsalar a Najeriya.