Wanda ake zargi da kisan ɗalibarsa Abdulmalik Tanko Ya musanta zargin hallaka ɗalibarsa da yin garkuwa da ita.

Lauyan malamin makarantar ne ya bayyana hakan a gaban kotu yayin da aka fara sauraron ƙarar a yau Litinin.
Gwamnatin Kano ta gurfanar da wanda ake zargi tare da thumarsa da aikata laifuka guda biyar wanda duk ya musanta zarge-zargen.

Daga cikin tuhume-tuhumen da gwamnatin Kano ke yi a kan waɗanda ake zargi akwai yin garkuwa, da neman kuɗin fansa da kuma kisan kai wanda ya musanta a zaman kotun na yau.

Tuni mai shari’a ya ɗage sauraron ƙarar zuwa ranar 2 da 3 ga watan Maris domin ci gaba da sauraron ƙarar.
A zantawar da yan jarida su ka yi da wanda ake zargi kafin gurfanar da shi a gaban kotu ya amsa cewar shi ya yi garkuwa da Hanifa Abubakar, sannan ya yi amfani da maganin ɓera wajen kashe ta wanda daga bisani kuma su ka binneta a cikin makarantar.
Mutane uku ake zargi da hada kai wajen aikata laifin wanda a yau su ka musanta a gaban kotu.
Gwamnatin Kano ta sha alwashin tsayawa tsayin daka domin ganin an gudanar da shari’ar cikin hanzari tare da goyon baya a kan hukuncin da kitu ta yanke wa wadanda ake zargi.