Wasu da ake zargi yan bindiga ne sun yi garkuwa da wasu mutane 22 a jihar Kaduna.

Al’amarin ya faru ne a Kajuru da misalin ƙarfe 12:30 na daren jiya.

Maharan sun shiga ƙauyen Idon tare da jikkata mutane huɗu sannan su ka yi awon gaba da wasu 22.

Babu rahoton rasa rai a sanadin harin da su ka kai a daren jiya.

Wani mazaunin garin ya tabbatarwa da yan jarida cewar ba su san adadin yan bindigan da su ka shiga garin ba illa kawai ƙarar habe-harbe da su ka ji sai kuma ƴan bindiga da su ka fara ɓalle ƙofofin gidajen mutane su na shiga.

Hukumar kula da al’amuran tsaro a Kaduna ba ta ce komai a dangane da harin ba.

Daga bangaren ƴan sana sun ce sun ka wasu mutane biyu da ake zargi da yin garkuwa da mutane da kuma sauran ta’addanci.

Mai magana da yawuun ƴan sandan jihar ,Muhammad Jalige ne ya tabbatar da hakan ya ce sun kama mutanen a ranar Talata.

Ya ce jami’an su sun kama mutanen a ƙauyen Sabon-Gaya da ke ƙaramar hukumar Chikun ta jihar Kaduna.

Leave a Reply

%d bloggers like this: