Bayan wani horo mai zurfi na tsawon wata guda akan harkokin kasuwanci, gwamnan jihar Borno, Farfesa Babagana Umara Zulum, a ranar Juma’a ya bai wa wasu matasa 152 tallafin naira miliyan  100  domin su dogara da kansu.

Gwamnan y aba wa matasan ne waɗanda su ka tuba daga ɗabi’ar daba.

Gwamnan ya bayar da tallafin ne a kwalejin fasaha ta Ramat da ke Maiduguri babban birnin jihar Borno.

Gwamnan y ace matasan da aka bai wa tallafin sun samu horo a kan sana’o’in dogaro dakai daban-daban sannan gwamnatin ta ga dacewar basu jari domin su dogara da kansu.

Gwamnatin jijhar Borno ta haramta ayyukan daba a jihar baƙi ɗaya tun a shekarar 2019 wanda ta haramta a sakamakon illata lafiya da ma rasa rayuka da ake samu a sanadiyyar faɗan daba a jihar.

Bayan haramta harkar daba a jihar Borno gwamna Zulum ya ƙaddamar da shirin horas da matasan sana’o’I daban-daban domin su dogara da kansu.

Gwamnan ya ce tallafin da gwamnati ke bayarwa yana karkashin sharadin cewa babu daya daga cikinsu da zai  koma dabar siyasa a jihar, yayin da kuma ana bukatar su biya rabin abin da suka karba.

Leave a Reply

%d bloggers like this: