Wasu da ake zargi ƴan bindiga ne sun sace wasu ango da amarya sannan su ka kashe yan sanda biyu a jihar Anambra.

Al’amarin ya faru a Okija da ke ƙaramar hukumar Ihiala ta jihar a ranar Litinin.
Mutane biyun da aka sace na kan hanyar zuwa filin sauka da tashin jiragen sama don yin tafiya.

Yan bindigan ba su magantu a kan buƙatar su kafin sakin mutane biyun da su ka sace ba.

Rahotanni sun nuna cewar an raunata direban motar su wanda a halin yanzu ya ke kwance a gadon asibiti don karɓar kulawar likitoci.
Mai magana da yawun yan sandan jihar Ikenga Tochukwu bai tabbatar da faruwar lamarin ba wanda ya ce bai samu rahoto daga jami’an su da ke yankin ba
Sai dai wani babban jami’in ɗan sanda da ya buƙaci a ɓoye sunan sa ya tabbatar da faruwar lamarin.
Al’amarin garkuwa da mutane na ci gaba da yawaita a kudu da arewacin Najeriya.