Ƙungiyar dillalan man fetur a Najeriya IPMAN ta bayyana dalilai da ya sa aka ƙara farashin man fetur a wasu daga cikin gidajen mai a Najeriya.

Shugaban ƙungiyar na yanin Benin guda cikin cibiyoyin da ake siyo man fetur Douglas Iyike ne ya sanar da haka a yayin da ya ke yi wa ƙungiyar ma’aikatan da su ke aiki a gidajen mai a Najeiya jawabi a dangane da wahalar mai da ake fama da ita.

Ya ce ƙarin farashin ya fara ne daga cibiyar da ake siyo man fetur wanda aka samu ƙarin farashin sa.

Ƙungiyar ta ce su na siyar da man fetur din ne la’akari da yadda su ka siyo shi daga cibiyar da su ke siyowa.

Samun ƙarin farashin man daga inda su ke siyo man fetur ɗin ne ya sanya wasu daga cikin gidajen mai ƙara farashin man fetur din.

A halin yanzu wasu daga cikin gidajen mai a Najeriya su na siyar da man fetur a kan kudi naira 200 zuwa 300 a kan kowacce lita.

A baya gwamnatin tarayya ta yi yunurin ƙara farashin man fetur zuwa nara 380 wanda ƙungiyar ƙwadago da sauran ƴan ƙasar su ka ƙi aminta da hakan.

Mutane na nuna damuwa a kan yadda farashin man fetur din ke hawa tare da ƙarancinsa, sai dai duk da haka kamfanin mai a Najeriya NNPC ya ce zai wadata ƙasar da man fetur din ba da jimawa ba.

A cewar kamfanin, ya shirya wadata ƙasar da isashen mai da ya haura lita biliyan biyu domin samawa ƴan ƙasar sauƙi.

Leave a Reply

%d bloggers like this: