Babban hafsan hafsoshin tsaron Najeriya Janar Lucky Irabor ya tabbatar wa ‘yan Najeriya cewa a shekarar 2022 za a samu zaman lafiya a duk sassan kasar da ake fama da rikici.

Irabor ya ba da wannan tabbacin ne a yau Asabar a Abuja a wajen taron majalisar wasannin soja ta duniya na 2022 na Ranar Rundunar Sojoji da Jami’an tsaro wanda aka yi wa take da “Running For World Peace” a bana.
Ya ce duniya na bukatar zaman lafiya wannan lokaci idan aka yi la’akari da yadda ake takun saka tsakanin Rasha da Ukraine da kuma kalubalen tsaro daban-daban da ke fuskantar Najeriya.

A cewarsa zaman lafiya na kara dawowa a sassa daban-daban na Najeriya kuma jami’an na taka rawar gani wajen tabbatar da hakan a ko da yaushe.

Irabor ya ce an gudanar da atisayen ne don taimakawa ma’aikatan don ƙarfafarsu tare da kasancewarsu cikin koshin lafiya domin ba su damar ci gaba da aikin samar da tsaro a faɗin ƙasar.
“Bayan haka, yana kuma taimaka wa jami’an wajen inganta lafiyarsu” a cewar sa.
Kamfanin dillancin labaran Najeriya NAN ya ruwaito cewa an fara tattaki da gudu na kilomita biyar ne a Aguiyi Ironsi Cantonment, Asokoro, Abuja ta Yakubu Gowon Barracks aka kare a Aguiyi Ironsi Cantonment.
An zabo waɗanda su ka raya ranar daga cikin sojoji, ’yan sanda, da sauran hukumomin tsaro.