Duk da sha’awar da ƴan Najeriya su ka nuna wajen taimakawa ƴan Ukraine a fagen daga gwamnatin Najeriya ta haramtawa yan ƙasar zuwa.

Gwamnatin tarayyar Najeriya ta ce ba za ta bar ƴan kasar domin zuwa taimakawa ƙasar Ukraine da ke yaƙi da Rasha ba.

Ma’aikatar harkokin ƙasashen waje ce ta sanar da haka a wata sanarwa da mai magana da yawun ma’aikatar ya santawa hannu.

Sanarwar ta ce ta dakatar da hyan ƙasar masu shirin ɗaukatr makami da nufin zuwa ƙasar Ukraine domin taimaka musu wajen yaƙi da Rasha.

Gwamnatin ta ɗauki wannan matakin ne yayin da ta ankara da wasu yan ƙasar da su ka yi dafifi a ofishin jakadancin Ukraine a Abuja domin yi musu rijista.

Yayin da ma’aikatar ƙasashen waje ta tuntuɓi ofishin jakadancin Ukraine a Najeriya, sun tabbatar da hakan wanda su ka ce akwai yan Najeriya da su ka je tare da nuna sha’awarsu na zuwa don taimakawa Ukraine a yaƙin.

Sai dai ofishin jakadancoin ya musanta raɗe-radin da ake na cewar ƙasar Ukraine za ta samar da bisa da kudin jirgi ga masu sha’awar taimaka musu a fagen daga bayan an biya dala dubu ɗaya kacal.

Gwamnatin tarayyar Najeriya ta ce za ta ci gaba da tuntuɓar ofishin jakadancin Ukraine domin tabbatar da dokar hana yan ƙasar zuwa Ukraine da nufin taimaka musu a fagen yaƙi.

Leave a Reply

%d bloggers like this: