Daga Ishaq Muttaka Magashi

Ba wani sabon abu ba ne idan a ka sake nanata wa mutane irin tallafawa rayuwar matasa da mata da Kwamishinan Kananan Hukumomi na Jihar Kano, Murtala Sule Garo ke yi a wannan mulkin na Maigirma Gwamna Abdullahi Umar Ganduje.

Mu matasa ‘yan Kano mazauna jihohin Arewa Ta Tsakiya na Najeriya, baya ga bibiyar ayyukan raya kasa da Kwamishina Murtala Garo yake yi a daukacin kananan hukumomi 44 na Jihar, mun shaida tare da misalai barkatai, na yadda ya yi fice wajen tallafawa rayuwar matasa da masu karamin karfi da kuma marasa aikin yi.

Ba tare da wani cika baki ba, mu na sanarwa mai karatu cewar, ya je ko ya sa a duba masa a ga yadda ofis din Garo ke cika duk lokacin da a ka ce ya na cikin ofis. Mutane ne kawai daruruwa ke yin tururuwa wajen ganinsa. Daga masu maganar ayyukan al’umma sai masu kai masa bukatun kansu. Hatta a gidansa ma mutane ne ke yin tururuwa.

Kullum maganar Murtala Garo ita ce mutane, musamman matasa, su tsaya da kafarsu. Ya kan ce musu “A kama sana’a ‘yan uwana, zaman banza ba namu ne ba.”

Mu fa a wajenmu ba aibu ba ne wai dan Jami’ai sun gayyace shi dan tattauna yadda za a kara samar da zaman lafiya a wannan jiha ta mu. Ganin yadda harkokin siyasa ke kara kankama a wannan jiha ta mu.

Mai kishin matasa da al’umma shi ke da dabarun sanin yadda za a gyara rayuwar matasan. Wannan ko shakka babu. Mutumin da a ke masa kirari da Kwamandan tabbatar da Adalci da kuma ci gaban jama’a, menene kuma sabo a wajensa a harkar siyasa a yanzu haka?

A matsayinmu na ‘yan Kano samari mazauna jihohin Arewa Ta Tsakiya na kasar nan, mu na kara jaddada fatan alherinmu ga Murtala Sule Garo da yunkurinsa na ganin an magance zaman banza tsakanin al’umma musamman mata da matasa. Saboda inganta harkar tsaro a wannan kasa ta mu.

Mu na kuma tare da yabon da Gwamnan Kano Ganduje ya yi wa Murtala Garo kwanan baya yayin wani taron wata mashahuriyar kungiyar kawo ci gaban al’ummar mazabar Majalisar Dattijai na Kano Ta Arewa. Wanda a ka yi taron a dakin taro na Africa House a gidan gwamnati. Baba Ganduje mu na godiya.

BA ABINDA ZA MU CE SAI MA RANAR KAWAI !!!

Daga Ishaq Muttaka Magashi
Shugaban Kungiyar Samarin ‘Yan Kano Mazauna Jihohin Arewa Ta Tsakiya

Leave a Reply

%d bloggers like this: