Rundunar ta ce ta ƙato wasu kekuna daga mayaƙan, sannan ta kashe goma daga ciki tare da ƙwato makamai a hannunsu.

Rundunar sojin Najeriya ta ce ta hallaka ƴan bindiga 100 a yankin arewacin ƙasar.
Mai magana da yawun rundunar a Najeriya Benard Onyeuko ne ya sanar da hakan a yau Alhamis lokacin da ya ke ganawa da manema labarai.

Ya ce dakarun soji na Hadarin Daji da sauran jami’an tsro sun hallaka ƴan bindiga 90 tare da ƙato wasu shanu 574 daga hannun yan bindiga.

Ya ƙara da cewa sun ƙwato makamai aga hannun ƴan bindiga daga ciki kuwa akwai bindigu ƙirar AK47 da harsashi mai yawa.
Sannan a yankin arewa maso gabas jami’an sojin sun hallaka mayaƙan Boko Haram 10 a jihar Borno tare da ƙwato wasu makamai daga wajensu.
Haka kuma rundunar ta ce ta ƙato wasu kekuna daga hannun mayaƙan Boko Haram a jihar Borno.
Rundunar ta ce ta samu dukkan nasarorin ne cikin makonni biyu da su ka gabata.