Wasu da ake kyauta zaton ƴan bindiga ne sun kai hari garin sarkin Pawa a ƙaramar hukumar Munya ta jihar Neja tare da sace wasu masu ibada a cikin wata coci.

Ƴan bindigan sun yi garkuwa da limamin cocin da kuma wasu mutane 44  na cikin garin.

An yi garkuwa da limamin cocin a kan hanyarsa ta zuwa Sarkin Pawa yayin da ya tsere wa harin ƴan bindigan zuw Gwada.

Al’amarin ya faru ne a ranar Lahadi yayin da ƴan bindigan su ka shuga garin Sarkin Pawa a jihar Neja.

Wani amzaunin garin ya shaida cewar mutane 44 da aka sace na daga ckin mutanen da aka mayar da su ƙauyukan su bayan sun baro sansanin ƴan gudun hijira.

Ya ƙara da cewar yayin da ƴan bindigan su ka kai harin sun kasance su na ci gaba da zirga-zirga a babban tinin ba tare da tsoro ko fargabar jami’an staro ba.

Ƴan bidnigan sun fara kai harin farko tun  a ranar Asabar yayin da su ka yi awon gaba da wasu dabbobi masu yawa, daga bisani kuma ranar Lahadi su ka koma sannan su ka sace ƴan gudun hijira bayan sun koma gidajensu.

Leave a Reply

%d bloggers like this: