Mutane 45 daga cikin mayaƙan ISWAP ne su ka rasa rayukansu yayin da mayaƙan Boko Haram su ka farmakesu a a raewa maso gabashini yaka da ƙasar Chadi.

Harin da mayaƙan Boko Haram su ka kai musu ya faru ne a ranar 28 ga watan Maris ɗin da mu ke ciki bisa jagorancin Muhammed Ari.

Wanda ya jagoranci kai harin kwamdandan Boko Haram ne a yankin Yauma Wango da Ngaama a ƙaramar hukumar Abadam ta jihar Borno.

Wani mai sharhi a kan al’amuran staro a yankin ya tabbatarwa da jaridar Leadership hakan wanda ya ce ya samu wani bidiyo na tsawon mintuna huɗu wanda aka hango mayakan ISWAP na binne ƴan uwansu.

Sannan akwai wani bidiyo da aka hango mayakan Boko Haram sun jera mayaƙan ISWAP bayan sun rufe fuskarsu da jan ƙyalle sannan su ka harbe su.

An fara takun saƙa tsakanin mayaƙan Boko Haram da na ISWAP bayan da manufa da ra’ayi su ka bambanta wanda hakan ya sa su ka yi silar mutuwar tsohon shugaban Boko Haram Abubakar Sheƙau.

Leave a Reply

%d bloggers like this: