Rundunar ƴan sanda a jihar Jigawa ta kama wasu mutane biyar da ake zargi da hannu wajen yin garkuwa da mutane.

An kama mutanen da ake zargi da aikata fashi da makami da kum agarkuwa da mutane a ƙaramar hukumar Ringim ta jihar.

Mai magana da yawun ƴan sandan jihar ne ya bayyana wa manema labarai hakan yau Litinin.

Ya ce an kama mutanen su biyar kuma ana zargin su da aikata fashi da garkuwa da mutane da aka yi a jihar.

Daga cikin waɗanda aka kama akwai Yusif Wakili wanda aka fi sani da Rago, sai Tahir Zango da Sabo Abdullahi sa aka fi sani da Sabo Gara sai Suleman Garba da ake kira Manu Dogo sai Inusa Jibril..

Jami’in hulɗa da jama’a na rundunar ya ce a halin da ake ciki yanzu su na ci gaba da samun bayanai daga ɓangaren wadanda ake zargi.

Sannan kuma za a miƙa waɗanda ake zargi a gaban kotu da zarar an kammala bincike a kan su.

Leave a Reply

%d bloggers like this: