Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya sha alwashin ɗaukar mataki tare da sake dabarun yaƙi a Najeriya musamman a yankunan arewa ta tsakiya da arewa ta yamma.

Muhammadu Buhari ya bayyana haka ne a ranar Laraba yayin ganawa da ƴan majalisar zartarwa na jam’iyyar APC  a fadar shugaban ƙasa da ke Abuja.

Ya ce ƙoƙarin da gwamnatinsa ta yi na samar da tsaro a yankin arewa maso gabas da yankin kudu maso kudu zai za a yi amfani da shi wajen magance matsalar tsaro a yankunan da ake fuskanta.

Sannan ya sha alwashin sake bibiyar yanayin tsarin gudanarwar ayyukan jami’an tsaro tare da sake ɗaukan sabbin matakai domin kawo ƙarshen matsalar tsaro.

Shugaba Buhari ya ce  babbar matsalar tsaro da ake fuskanta a yankin arewa maso yamma da arewa ta tsakiya  nan ba da jimawa ba zai zama tarihi.

Shugaban ya ce idan aka yi duba a arewa maso gabas akwai nasarori da aka samu  masu yawa la’akari da ƙananan hukumomin da su ke hannun mayaƙan Boko Haram da kuma nasarar da aka samu a

gwamnatinsa.

 

 

A wani labarin kuma shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya karɓi baƙoncin babban mai gabatar da ƙara a kotun masu laifi ta duniya.

Shugaban ya karɓi bakoncin Karin Ahmad Khan a fadarsa da ke Abuja ranar Laraba.

A yayin ziyarar da babban mai gabatar da ƙara a kotun masu manyan laifuka ta duniya, shugaban ya tabbatar da cewar a halin da ake ciki ƴan Najeriya sun tabbatar da cewar mayaƙan Boko Haram ba jihadi su ke yi ba.

Ya ce tsarin Boko Haram ya saɓa da na addinin musulunci wanda hakan ya fito ƙarara yan ƙasar su ka fahimta a yanzu.

Ya ce haramta karatun boko da mayaƙan ke yi ba daidai ba ne sanna  su na kashe mutanen da ba su ji ba ba su gani ba shi ya sa Najeriya ke yaƙar su kuma ake samun Nasara.

Shugaba Buhari ya ce a yayin da ya karɓi ragamar mulkin ƙasa abubuwan sun ƙazanta sai dai a yanzu an shawo ka mafi yawan ƙalubalen da aka fuskanta na Boko Haram a Najeriya.

A yayin jawabinsa babban mai gabatar da ƙara a kotun masu aikata manyan laifuka ta duniya Karin Ahmad Khan ya ce kotu ta gamsu da yadda aka yi hadaƙa a tsakanin ƙasashen da su ke iyaka da yankin tafkin chadi wajen yaƙar mayaƙan Boko Haram.

 

 

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya gana da manyan hafsoshin tsaron Najeriya yau Alhamis a fadarsa da ke Abuja.

Ganawar na zuwa ne bayan da ya sha alwashin sauya tsarin tafiyar da al’amuran tsaron Najeriya yayin wani taro da ya yi ranar Laraba.

Shugaban na tataunawa da manyan jami’an tsaron ƙasar domin su ba shi bayanai a kan halin da ake ciki a kan matsalar tsaron da ake fusknata.

Shugaban ya tattauna da jami’an tsaro da kuma wasu hukumomi masu alaƙa da tsaro a ƙasar.

Ganawar tamayar da hankali ne a kan halin da ake ciki na tsaro musamman yankin arewa maso yamma da arewa ta tsakiya.

Shugaba Buhari ya tabbatar da cewar za a sauya tsarin tafiyar da al’amuran tsaro a Najeriya wajne ganin an kawo ƙarshen ƙalubalen da kasar ke fuskanta na tsaro musamman a yankin arewa maso yamma da arewa ta tsakaiya.

 

 

Leave a Reply

%d bloggers like this: