Almajiranci/karatun Allo/Bara

Wallafawar Abubakar Murtala Ibrahim
(#Abbanmatashiya)
08030840149
Menene almajiranci?
Almajiranci kalma ce, aikatau, a kan laƙabawa wanda aka kai karatun allo wani gari ko wata ƙasa domin mayar da hankali wajen karantar alƙur’ani mai tsarki.
Karatun allo kuwa ya samo asali ne tun bayan da addinin musulunci ya wanzu a wasu sassan Afrika da ƙasa Najeriya musamman wasu jihohin arewaci.
Mutane na ɗaukar ƴaƴansu da su ka haifa tare da kai su wajen malami da ya karanci alƙu’ani domin ƙauna da soyayyar da su ke yi wa ƴaƴansu ta yadda za su zamto gangaran a fagen karatun addini wanda shi ne tushe.
Al’ummar arewa na ci gaba da ɗabbaga wannan al’ada domin girmama malamai na soro da kuma ƙarfafar ƴaƴansu don ganin sun kasance masu fahimtar Alƙur’ani mai tsarki.
Akwai abubuwa da dama waɗanda ke tattare a ƙarƙashin karatun allo wanda hakan ke koyar da mutane rayuwa ta dangana, dagewa, mayar da hankali da naci ba tare da nuna fifiko ba kasancewar dukkanin ɗaliban iri ɗaya ake ɗaukar su.
Mutanen da masu arziƙi ne sannan masu dukiya ne amma hakan ba ya hana ɗaukar ƴaƴansu domin kai su karatun allo wata ƙasar, ko jihar ko kuma unguwa.
Wasu daga cikin iyaye a wancen lokaci na ɗaukar kayan abinci tare da kai ziyara lokaci zuwa lokaci a makarantun da su ka kai ƴaƴansu domin nuna godiya da girmamawa sannan su san halin da ƴaƴansu ke ciki.
Kasancewar a baya akwai sauƙin al’amura musamman ɓangare abincin malaman kansu bas su damu da sai iyaye sun kawo abinci ba, domin da yawa daga cikin malaman na da gonaki waɗanda su ke nomawa sannan su ciyar da ɗaliban da ke gabansu ba tare da ƙyashi ko gajiyawa ba.
A kwana a tashi rayuwa ta fara sauyawa wanda ta kai wasu malaman sun tsinci kansu a cikin gari, babu gonakin da za su noma balle su iya ciyar da dukkan almajiran da ke gabansu wanda hakan ya sa mutanen unguwa ke iya ɗaukar masu taimaka musu daga cikin almajiran tare da ciyar da su.
Idan za a iya tunawa a baya kaɗan wato shekaru ƙalilan da su ka shuɗe za ka iske wasu almajirai na zaman siɗi musamman idan su ka ga magidanta na cin abinci bayan sallar magriba ko sallar isha’i.
Hakan ta ƙara matsewa rayuwa ta ƙara tsadar da ba a iya ɗaukar wannan ma, hakan ya sa wasu almajiran ke zuwa bara gida-gida domin samun abinci na wani lokaci a hakanma dai su na samu ko dai a gidan malamin su kuma a wani gida da su ke yin aikatau.
Baya ga wannan bara da su ke zuwa na wani lokaci domin samun abincin ko dai na rana ko na dare, a dukkanin ranakun Alhamis da Juma’a almajiran na zuwa cin kasuwa a ƙauyuka idan kuwa a cikin gari ne su na zuwa wasu kasuwani mafi kusa, a wancen lokacin ba bara su ke zuwa ba, su na yin ko dai dako, ko kuma yin wani aiki da za su sami wani abu da za su siyi sabulu don yin wanki, ko kuma wani abu kamar tawada, allo, alƙalami da sauransu.
Tsadar rayuwar da mu ke ciki a yau ta tilastawa wasu daga cikin malaman makarantun allo janye ranar Talata domin bai wa almajiransu dama don ci gaba da irin wancen aikatau domin samun kuɗin da za su cike giɓin da su ka rasa.

Mecece Bara, Kuma su waye su ke bara?

Bara wani aiki ne da mutane kan fita walau masu buƙata ta musamman, ko gajiyayyu (tsofaffi) ko kuma wasu daga cikin mutane marasa godiyar Allah.
Ko a zamanin baya shekarun da su ka gabata da wahala ka ga wasu mabarata ko dai daga ɓangaren masu buƙata ta musamman ko kuma mata da maza gajiyayyu sun yi nisan zango wajen yin ta.
Su na zuwa ranakun kasuwa, ko kuma gefen wata bishiya ko wata ƴar hanya da mutane ke zirga-zirga tare da yi wa masu tafiya addu’a ala-bashshi idan ka yi niyya ko ra’ayi ka bayar da sadaka a garesu.
A kan bai wa mutane masu buƙata ta musamman ko tsofaffi sadaka domin kwaɗayin addu’ar bakinsu.
A zamanin yau da mu ke ciki bara ta zamto tamkar sana’a, domin wasu na tasowa daga wasu ƙauyuka su taho bara, daga ciki kuwa akwai matan aure, zawarawa, da ƙananan yara maza da mata wanda wasu ɓata gari daga cikinsu ma ake lalata da su a cikin gari.
A wani bincike da na yi kwanakin baya na gano wasu mutane da suke zuwa ƙauyuka domin ɗakko yara haya da zumman kawosu birni bara, idan aka samu kuɗin ana kai wa iyayensu wani kaso daga abinda aka samu na barar.
Amma mu sani sannan mu fahimta, su irin waɗannan mutane da su ke zuwa domin yin bara, ba fa almajiranci su ke zuwa ba, sannan ba karatu su ke yi a gaban malaman allo ba, aa, barar dai su ke zuwa yi, a haka wasu idan idanunsu ya buɗe mazan sun fanɗare su fara shaye-shaye, wasu sace-sace, wasu kuma masu kishi daga ciki su dinga yin sana’ar dogaro da kai da ƴan buga-guga don rufawa kansu asiri.
Kun ga ke nan akwai bambanci tsakanin almajirin da ya ke gaban malami ya na karatun allo da kuma irin waɗancan da ake ɗakkowa haya don yin bara a cikin gari.
Har gobe akwai wannan al’ada ta malam bahaushe domin ɗaukar ƴaƴansu wajen kai su gaban malamai a wasu garuruwan domin karatun Alƙur’ani, amma sai aka sami wasu ko dai rashin sani ne ko kuma kwangila ce, sai su ke alaƙanta karatun allon da irin wannan barar da na fayyace muku domin kassara karatun da rage masa karsashi a idon duniya.

Ta yaya za a magance matsalar barar da ake cece-ku-ce a kanta?

Alhaki ne na gwamnati domin wasu jihohin na yin kamen almajirai tare da mayar da su gaban iyayensu.
To amma da ake kama almajiran, nawa ne su ke faɗar ga malamin da sju ke karatu a gabansa?
Za mu ga cewar adadin almajiran da ake kai wa ma ya ragu, amma almajiran da ke bara a cikin gari sun ninka tunanin mai lissafi.
Idan gwamnati ta so, za ta iya ɗaukar mataki na hana irin waɗancan mutane yin bara domin inganta tsaro, tarbiyya da kuma tsaftace jihohin arewa.
Akwai mutanen  a cikin garin su ke su ke zuwa ƙauyuka su na ɗakko yara ƙananan domin kawo su bara, wasu kuma a na kawo musu ne har inda su ke, to gwamnati ta bincika sai ta ga hanyar da ta fi dacewa domin kawo gyara a lamarin.
Amma ina mai tabbatar da cewar karatun Al’ƙurani daban ne, kuma ba wani abu da zai sauya daga yadda ake domin ba almajiran makaranta Alƙur’ani ne ke watangaririya a titi ba.
Idan rubutu na bai maka/miki daɗi ba don zan kashe muku kasuwar kwangila ku yi haƙuri.
Bissalam
Abubakar Murtala Ibrahim
#Abbanmatashiya
22 Ramadan 143
23 Afrilu 2022

Leave a Reply

%d bloggers like this: