Fadar sarkin musulmi a Najeriya ta ce ba a ga watan sallah ba a Najeriya.

Kwamitin ganin wata ya ce rahoton ganin wata da su ka samu a jihohin Legas da sauransu ba su inganta ba.
Wannan ke nuni da cewar za a yi sallah ne ranar Litinin.

Tuni hukumomi a ƙasar saudiyya su ka bayar da rahoton rashin ganin wata wanda gobe Lahadi za a cika azumi 30.
