Hukumar hana Cunkoson ababen hawa a jihar Kano KAOTA ta ce ta shirya tsaf domin ganin an hana cunkoso yayin bikin ƙaramar sallah.

Hakan na ƙunshe a wata sanarwa da mai magana da yawun hukumar Nabilusi Abubakar ya sanyawa hannu tare da raba wa manema labarai ranar Asabar.
Ya ce hukumar ta ware jami’anta guda 2,000 wadanda za su kula da zirga-zirgar ababen hawa a ciki da gefen jihar Kano yayin bikin ƙaramar sallah.

Sai dai hukumar ta ja kunnen masu amfani da lokacin bikin salah wajen yin ganganci da ababen hawa da cewar ba za ta lamunci hakan ba.

Sannan hukumar ta ce ba za ta zuba ido a bar ƙananan yara da shekarunsu bas u kai yadda za su yi tuƙi bas u hau titunan jihar domin hana cunkoso.
Hukumar ta ce a shirye ta ke tsaf domin ganin ta kama duk wanda ya karya doka tare da gurfanar da shi a gaban kotu domin yanke masa hukunci.