Ƙungiyar malaman jami’a a Najeriya ta sanar da janye yajin aikin gargaɗi da ta shiga.

Ƙungiyar ta sanar da hakan a shafinta na Tuwita.
Ƙungiyar ta ce malaman jami’a za su koma bakin aikinsu daga gobe Litinin sannan za ta ci gaba da duba yiwuwar tafiya yajin aikin sai baba ta gani a nan gaba.

Ƙungiyar ta shafe tsawon lokaci a yajin aikin, sai dai janye yajin aikin da su ka yi ba su yi wani karin bayani ko sun daidaita da ɓangaren gwamnati ba.
