Ƙungiyar malaman jami’a a Najeriya ASUU ta ce ba ita ta sanar da janye yajin aikin gargaɗi a shafin tuwita ba.

Wani cikin shugabannin wanda Mujallar Matashiya ta zanta da shi ya ce sam ba su da shafi a kafafen sada zumunta wanda su ke bayar da bayanai a kan abubuwan da su ka shafe su.

Wani shafi a Tuwita mai ɗauke da sunan ƙungiyar ne ya sanar da janye yajin aikin a yammacin yau Lahadi.

A halin da ake ciki ƙungiyar na gudanar da wani zama a Abuja domin tattaunawa a kan matsalolin da su ke fuskanta.

Watanni ƙungiyar ASUU ta shafe cikin yajin aiki duk da cewar ba ta cimma matsaya tsakaninta da gwamnati ba.

Leave a Reply

%d bloggers like this: