Ahmad Sulaiman Abdullahi

Aƙalla mutane 55 aka tabbatar sun rasa rayukansu a wasu sabbin hare-hare biyu da ƴan ta’adda suka kai yankunan ƙananan hukumomi biyu a Zamfara.

Mun samu rahoto cewa kusan mutum 48 ƴan ta’addan suka kashe a ƙauyukan Sabon Garin Damri, da Kalahe a ƙaramar hukumar Bakura.

Shugaban dake kula da yankin Bakura, Aminu Suleiman, wanda ya tabbatar da faruwar lamarin a ƙarshen makon nan, ya ce ƴan ta’addan sun shiga Sabon Gari da misalin ƙarfe 2:00 na rana ranar Jumu’a.
Rahoto ya nuna sun ƙashe mutane 9 a nan, kuma suka wuce garin Damri, inda suka yi ajalin wasu mutum huɗu ciki har da ɗan sanda da jami’in hukumar NSCDC.
Haka kuma ƴan ta’addan sun kai hari kan babura da yawa sun kuma ƙona Motar Hilux mallakin ƴan sanda.
Bayan haka maharan sun ƙara kashe mutum 8 a ƙauyen Kalahe, wanda ke tsakanin Sabon Garin Damri da kuma cikin garin Damri.
A cewar Sulaiman ƴan ta’addan ba su tsaya nan ba, sun farmaki Asibitin da ake duba marasa lafiya kuma suka kashe majinyata.
Sulaiman ya ƙara da cewa Sojoji sun shiga garin suka yi musayar wuta da ƴan bindiga, bisa tilas yasa ƴan Ta’addan suka sake koma wa Sabon Garin Damri bayan ƙashe mutum 9 da farko, suka koma suka kashe wasu 21.
Shugaban yankin ya tabbatar da cewa a dukkan hare-haren aƙalla mutane 48 ne suka rasa rayukansu.
Ƴan bindiga sun sake kai sabon hari a wani harin a ranar Asabar.
Wata majiya daga yankin Maradun ta bayyana cewa an sake kai hari kauyukan Faru da Minane, kamar yadda Channels tv ta ruwaito.
“Ina cikin babban Asibitin Maradun lokacin da sojoji suka kawo gawarwakin mutanen da aka kashe,” inji wani Jamilu Muhammad.
“Mutanen mu a ƙauyen Mutanen sun ce ƴan ta’adda sun shigo mintuna ƙafin ƙarfe biyu na rana, suka buɗe wuta kan mai uwa da wabi.”
A cewarsa, mutum shida aka kashe a ƙauyen yayin da wani mutum ɗaya ya mutu a Faru.
Ya ce adadin mutanen da suka mutu zasu iya ƙaruwa saboda mutane da dama sun bata.
Kakakin rundunar ƴan sanda reshen jihar Zamfara, Mohammed Shehu, be amsa kira ko sakonnnin da aka tura masa ta wayar salula ba.