Ahmad Sulaiman Abdullahi

 

 

 

Iyalan waɗanda aka sace a jirgin ƙasa a Kaduna, wanda ya taso daga Abuja Abuja sun yi zanga-zangar lumana a manyan titunan kaduna a yau Litinin.

Ƴan uwa da iyalan sun nuna damuwarsu kan rashin ceto ko sakin wadanda aka sacen.

Haka kuma iyalai da ƴan uwan waɗanda aka sacen sun gudanar da taron manema labarai a kan lamarin a Abuja.

A ranar 28 ga watan Maris ne, ƴan Ta’adda suka tayar da bam a kan layin dogo na jirgin, sannan kuma suka buɗe wa jirgin da ke cike da fasinjoji wuta, inda suka hallaka wasu sannan suka yi awon gaba da wasu.

A yau Litinin, su ka cika kwana 42 kenan dayin garkuwa da fasinjojin har yanzu ba a sako su ba.

Bayanai sun nuna cewa ƴan bindigan da saka sace su sun gabatar wa da gwamnatin tarayya wasu buƙatu kafin su saki mutanen.

Hukumomin Najeriya sunce suna iya bakin ƙokarin su wajan ganin sun kuɓutar da mutanen.

Haka kuma hukumomin ta ɗora alhakin harin a kan ƴan ƙungiyar Boko Haram.

Leave a Reply

%d bloggers like this: