Babban Lauya, kuma dattijon ƙasa, Cif Robert Clarke (SAN), ya yi kira da a ƙara wa shugaban ƙasa Muhammadu Buhari wa’adin mulki bayan kammala mulkinsa na biyu a 2023.

Babban lauyan, wanda ya bayyana hakan a jiya Litinin ɗin da ta gabata, ya bayyana cewa watannin da ke gabanin zaɓen 2023 ba su isa su kawo ƙarshen matsalar rashin tsaro da ake fama dashi ba, balle a iya zaɓe cikin kwanciyar hankali.

Ya bayyana hakan ne a yayin da yake zantawa da gidan talabijin na Arise.

Clarke ya ƙara da cewa kundin tsarin mulkin Najeriya ya tanadi cewa shugaban ƙasa zai iya tsawaita wa’adinsa na tsawon watanni shida, idan yana jin cewa gudanar da zaɓe zai iya zuwa da tasgaro.

Ya ce ba daidai ba ne a yi imani cewa Shugaban ƙasa ba zai iya ci gaba da zama a karagar mulki sama da shekaru takwas na wa’adin mulki biyu ba.

Clarke ya ce shugaban ƙasar na iya ƙara wa kansa wa’adin watanni shida domin a samu gudanar da zaɓe cikin lumana.

Leave a Reply

%d bloggers like this: