Hukumar kwastam ta sanar da nasarar data samu daga tsakanin watan Maris zuwa Afrilun 2022 a jihohin kano da Jigawa.

Hukumar ta bayyana adadin kayayyakin data kama wanda kuɗin su yakai kusan naira biliyan biyu.

Sanarwar ta fito daga hannun, kwanturolan hukumar da ke kula da Kano da Jigawa MA Umar, a yayin wani taron manema labarai a Kano.

Nau’in kayan sun haɗa da katan 3,387 na shinkafa ƴar waje da gwanjo da taliya da miyagun ƙwayoyi da sauran.

Ya kuma bayyana cewa rundunar da yake jagoranta ta samu ƙarin kuɗin shiga da take samu daga biliyan 9.6 zuwa biliyan 14 cikin watanni biyu.

Leave a Reply

%d bloggers like this: