Wasu da ake zaton yan bindiga ne kan babura sun farmaki kauyen Taka Lime da ke karamar hukumar Goronyo a jihar Sokoto inda suka kashe mutane takwas tare da yin garkuwa da wasu da dama.

Wani mazaunin kauyen Taka Lime, wanda aka kashe matarsa da diyarsa a harin, Sani Takakume, ya ce yan bindigar sun farmaki kauyen ne inda suka yi ta harbi kan mai uwa da wabi.
Ya ce “mun fito kwanmu da kwarkwatanmu dauke da makamai daban-daban don tunkarar maharan kuma mun yi nasarar kashe uku daga cikinsu sannan mun kama daya.”

“Da suka gane cewa mazauna kauyen sun kashe uku daga cikinsu, sai suka kashe takwas daga cikin mutanen da ke tsare a hannunsu a matsayin ramuwar gayya.”

Ya ce abun bakin ciki shine cewa daya daga cikin yan bindigar ya zauna a cikinsu a kauyen tare da iyayensa.
Rahoton ya kara da cewa yan bindigar sun riga sun bukaci a biya naira miliyan 10 a matsayin kudin fansar wasu daga cikin mazauna kauyen da aka sace sannan a biya wani naira miliyan 10 haraji kan al’ummar garin gaba daya idan har suna son a samu zaman lafiya a kauyen.