Shugaban Kwamitin Majalisar Dattawa mai kula da harkokin sufurin jirgin kasa, Sanata Abdulfatai Buhari, ya nuna damuwarsa a kan yadda aka kasa ceto wadanda harin jirgin kasan Abuja zuwa Kaduna, ya rutsa da su tsawon kwanaki 47.

Sai dai Sanatan ya yi kira ga gwamnatin kasar China da ta sa hannu aciki domin gaggauta ceto wadanda abin ya shafa.
Ya yi wannan jawabi ne a yayin wata ziyarar kwamitin hadin gwiwa na Majalisar Dokoki ta kasa kan sufurin jirgin kasan Legas zuwa Ibadan.

Dan majalisar, wanda ke wakiltar Oyo ta Arewa a Majalisar Dattijai, ya ce lamarin da ya faru a ranar 28 ga watan Maris, ya jefa kokonto ga ’yan Najeriya da suka fara rungumar jirgin kasa a matsayin hanyar tafiye-tafiyensu.

Ya ce babu laifi idan gwamnatin kasar China ta taimaka wa Najeriya domin ceto wadanda lamarin ya shafa.
Daily Trust ta rawaito cewa, titin jirgin kasan Abuja zuwa Kaduna mai tsawon kilomita 159, wani katafaren kamfanin gine-gine na kasar China, wato CCECC ne ya gina shi, kuma Bankin Kasar China ne ya bayar da kayayyakin titin.
Ya ce idan wadanda ke cikin dajin na bukatar lamuni, China za ta iya shige wa gaba, inda ya kuma ya bukaci hukumar CCECC da ta mika sakon ga gwamnatin kasar China don taimaka wa Najeriya.
Sanatan ya kara da cewa, idan har kasar China za ta iya taimaka wa kasar Rasha a yakin da ta ke yi da Ukraine, babu laifi wajen taimakon Najeriya a halin da ta ke ciki ayanzu.