Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya bukaci masu neman mulki a siyasa su sauka daga mukamin da su ke.

Shugaban ya nemi masu rike da mukamai a gwamnatinsa su sauka yau yayin zaman majalisar zartarwa a fadarsa da ke Abuja.

Ministan yaɗa labarai da al’adu Lai Mohammed ne ya sanar da haka yayin da ya ke yi wa maneman labarai karin haske bayan kammala zaman majalisar.

Shugaban ya bai wa ministocin da su ke neman kujera su sauka daga mukaminsu zuwa ranar 16 ga watan Mayun da mu ke ciki.

Akwai ministoci da dama a gwamnatinsa da su ke neman kujerar shugabancin kamar ministan sufuri Rotimi Amaechi, ministan kwadago Christ Ngige da minsitan shari’a Abubakar Malami sannan ministan Naija Delta Godwill Akpabio.

Leave a Reply

%d bloggers like this: