Hukumar zaɓe mai zaman kanta ta Ƙasa (INEC) ta ce za ta dakatar da aikin rajistar kada ƙuri’a ta yanar gizo a ranar 30 ga watan Mayu.

Hukumar ta INEC a baya ta ce za a ci gaba da gudanar da rijistar ta yanar gizo da kuma ofishi a lokaci guda har sai an dakatar da aikin CVR a ranar 30 ga Yuni, 2022.

Amma shugaban INEC
Farfesa Mahmood Yakubu, ya ce za a kawo karshen yin rijistar ta yanar gizo a watan Mayu.

Shugaban ya bayyana hakan a ranar Laraba a taro karo na biyu na watanni uku da ƙungiyoyin farar hula na 2022.

Ya ce hakan zai bai wa waɗanda suka yi rajista ta yanar gizo lokaci domin su kammala rajistarsu a ofishi kuma zai ba hukumar damar tsaftace bayanan rajistar.

A cewarsa:

“Kamar yadda kuka sani, rijistar masu kaɗa kuri’a (CVR) da ke ci gaba da gudana zai zo ƙarshe a wata mai zuwa watau 30th June 2022.

Duka rijista ta yanar gizo da kuma rajista a cibiyoyin da aka keɓe suna gudana lokaci guda.”

Leave a Reply

%d bloggers like this: