Ƴan ƙungiyar sa kai a Jihar Neja sun kai farmaki sansanin ƴan fashin daji tare da ceto mutum 17 da aka yi garkuwa da su a Dajin Zago.

Wani da aka gudanar da aikin da shi ya nemi ɓoye sunansa ya tabbatar da ceto mutanen fadar basaraken Etsu Yaba da ke Abaji, Alhaji Abdullahi Adamu.

Inda aka kai mutanen Yankin Zago na maƙwabtaka da Ƙaramar Hukumar Abaji da Birnin Tarayya Abuja anar Alhamis.

“Mun shirya mu da kanmu kuma muka shiga dajin, amma da suka gan mu sai suka fara harbe-harbe.

Mu kuma har sai da muka kai wajensu, Sai kuma suka fara guduwa,” in ji shi.

Ya ƙara da cewa: “Mun ga mutum 17 a ɗaure, muka kwance su, muka ɗebo bindigogi kuma muka kawo wa mai martaba Etsu Yaba.”

Sarkin ya yaba wa dakarun, yana mai cewa “korar ƴan fashin za ta daɗaɗa wa mazauna masarautarsa tare da ci gaba da ayyukansu na noma cikin kwanciyar hankali”.

Leave a Reply

%d bloggers like this: