Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya sha alwashin taimakawa ƙasar Sudan Ta Kudu domin yaƙi da ƴan bindigan da su ka addabeta.

Shugaban ya bayyana hakan ne yau Juma’a lokcin da yak e karɓar baƙuncin wakilin shugaban ƙasar Sudan ta Kudu a fadarsa da ke Abuja.
Shugaban y ace za a duba yiwuwar taimakawa ƙasar Sudan ta Kudu wajen yaƙi da ƴan bindigan da su ka addabi ƙasar.

Wakilin shugaban Sudan Ta Kudu yay i wa shugaba Buhari bayanin bullar wata ƙungiyar mai kama da Boko Haram da ta ke neman addabar ƙasar.

A wata sanarwa da mai magana da yawunsa Femi Adesina ya fitar, ya ce wakilin shugaban Sudan Ta Kudu ya buƙaci a kawo jami’an tsaro ta don basu horo a Najeriya.
Shugaban ya ce zai duba halin da su ke ciki tare da kallon hanyar da za a taimaka musu.