Anyi arangama tsakanin jami’an tsaro da matasa a garin Sokoto, inda matasa ke ci gaba da zanga-zangar kan kalaman ɓatanci da ya jawo kisan wata matashiyar ɗaliba mai suna Deborah Samuel.

Matasan maza da mata suna gudanar da zanga-zangar a wurare daban-daban a faɗin Sokoto tare da ƙona tayoyi, da suka haɗa da Fadar Sarkin Musulmi Alhaji Sa’ad Abubakar III.

Kazalika wasu sun yi cincirundo a ƙofar gidan gwamnatin jihar.

Masu zanga-zangar na neman jami’an tsaro su saki mutanen da suka kama da ake zargi da kisan matashiyar da ke karatu a Kwalejin Ilimi ta Shehu Shagari, wadda ake zargi da zagin Annabi Muhammadu (SWA).

Rahotanni sun sun bayyana cewa da farko matasa na gudanar da zanga-zangar cikin lumana.

Daga bisani sai ta rikide ta zuwa tamkar rikici, inda mutane suka dinga jefa duwatsu kan gidan sarkin Musulmin.

Wani da ke kusa da fadar sarkin a lokacin da abin ya faru ya shaidawa manema labarai cewa jami’an tsaro sun yi ƙoƙarin dakatar da matasan kutsawa fadar.

Ya ƙara da cewa “da yawa yaran masu zanga-zanga na ganin sarkin ya goyi bayan yarinyar (Deborah), shi ne suke jefe-jefe.

Kazalika wani Shi ma wani mai suna Murtala ya tabbatar da haribin mutum biyu cikin masu zanga-zangar.

yace har zuwa lokacin haɗa wannan rahoton matasan na ci gaba da jifa, su kuma jami’an tsaro na harbi.

Ya kuma bayyana cewa an kama mutane da dama, a cewarsa.

Leave a Reply

%d bloggers like this: