Hukumar yaƙi da rashawa da cin hanci EFCC ta gurfanar da lauya da abokansa gaban babban kotun tarayya dake Uyo, jihar Akwa Ibom.

EFCC ta gurfanar da lauya da wasu mutum shida kan haɗa baki wajen wawure kimanin milyan goma sha huɗu na wani ɗan sandan da ya mutu.
Hukumar ta bayyana hakan a jawabin da ta saki a shafinta na yanar gizo a jiya ranar Juma’a.

Matar ɗan sanda tayi gaggawa kai ƙara wajen ƴan sanda an kwashe mata kuɗin gadon da mijinta ya bari.

A cewarta, matar ɗan sandan ta shigar da ƙara kan yadda aka kwashe kuɗi milyan 13 dake asusun ɗan sanda wanda babban sufritanda ne kafin mutuwarsa.
Cikin jawabin da hukumar ta fitar ya bayyana cewa:
“Sashen EFCC na Uyo ta gurfanar da da Barista Samuel Ebitu tare da mutum shida, kan laifin sace N13,171,415.25 daga asusun bankin mataccen ɗan sanda.”
“An gurfanar da mutanen a gaban Alkali Agatha Okeke.”
“Sauran mutum shidan sun haɗa da Etimbuk Godwin Edet, Michael Jeremiah Isong, Sunny Isong, Godwin Ekanem, Emmanuel Jackson Isong da Harrison Ofuomah Emamoke.
Hukumar ta bayyana cewa matar marigayin ce ta shigar da ƙara kan yadda suka wawure kuɗin gadon da mijinta ya bari.