Ƴan bindiga da ake zaton masu garkuwa da mutane ne sun kwashe matafiya da dama a kan sananniyar hanyar Kaduna zuwa Abuja ranar Talata.

Wani shaidan gani da iso ya faɗa wa manema labarai cewa maharan sun kai harin ne da misalin ƙarfe 4:30 na yammacin ranar a ƙauyen Katari da ke kan hanya.

Shaidan ya ƙara da cewa yanzu haka akwai motocin matafiya da dama da suke ajiye a kan hanyar zuwa da kuma dawowa daga Kaduna.

Maharan sun tattara mutanen daga bisani su ka yi gaba da mutanena.

A cewarsa sai bayan maharan sun gama cin karensu ba babbaka, sannan jami’an tsaro masu yawa suka dira wurin domin kawo ɗauki.

Rahoton da muka samu ya bayyana cewa ƴan bindigan dajin sun tare babbar hanyar ne a dai-dai ƙauyukan Kurmin Kare da Katari, ƙaramar hukumar Kachia, jihar Kaduna, inda suka sace matafiya a motocin haya da na gida.

Wata majiya daga ƙauyen Katari ta ce tun da safiyar Talata, maharan suka farmaki garin suka sace mutum 16, da yamma kuma misalin karfe 4:00 da motsi suka toshe hanya.

Kakakin ƴan sandan Kaduna, ASP Mohammed Jalige, ya ce har yanzun ba samu tabbaci ba daga kwamandan da ke aiki a yankin.

Leave a Reply

%d bloggers like this: