Hakimin Karfi da ke karamar hukumar Takai a jihar Kano, Abdulyahyah Ilo da aka sace ya shaƙi iskar ƴanci daga hannun ƴan bindiga da suka yi garkuwa da shi.

Masu garkuwan, sun riƙe karamin farfesa a Jami’ar Kimiyya da Fasaha ta Jihar Kano (KSTU), Wudil, Huzaifa Karfi, wanda rahotanni suka ce ya je ne domin kai kuɗin fansa.

Rahotanni da muka kawo muka a baya kunji cewa ƴan bindigan sun kashe mutane shida da suka yi ƙoƙarin ceto basaraken ƙauyen a lokacin da suka yi awon gaba da shi.

Cikin rahotan kunji cewa sun mamaye ƙauyen ne a kan babura daga jihar Bauchi ta dajin Ringim da ke Jigawa.

Wani mazaunin yankin mai suna Musa Sa’ad ya tabbatar da sakin basaraken da masu garkuwa da mutane suka yi.

Ya bayyana cewa mafarauta da ƴan banga sun kama wani da ake zargin mai garkuwa da mutane ne a cikin daji da ke da nasaba da sace-sace a ƙauyen Karfi.

A cewar majiya:

“Sun karɓi kuɗin fansa tare da tsare Dr Huzaifa saboda da mutumin da mafarauta da ƴan banga suka kama.

Sun buƙaci a sako mutumin nasu a matsayin sharaɗin sakinsa.”

Wani ɗan uwa ga sarkin gargajiyan, Yusuf Ismail ya tabbatar da cewa an sako basaraken kuma yana jinya a asibiti.

Da aka tuntubi kakakin rundunar ƴan sandan Jihar Kano, SP Abdullahi Kiyawa, yace a halin yanzu bashi da abin cewa akan lamarin, amma ya yi alkawarin ba da bayani idan ya samu.

Leave a Reply

%d bloggers like this: