Rahoton da rundunar sojin Najeriya ta fitar ya bayyana yadda ƴan ta’addan Boko Haram ke ci gaba da mika wuya ga gwamnati.

Hedikwatar tsaro ta najeriya a jiya ta ce ƴan ta’addan Boko Haram 53,262 ne suka mika wuya.

Hedkwatar ta ce akalla ƴan Boko Haram 1,627 ne da iyalansu, waɗanda suka haɗa da maza 331, mata 441 da ƙananan yara 855, sun mika wuya ga sojojin a wurare daban-daban tsakanin 1 ga Mayu zuwa 14 ga Mayu.

Darakta, Ayyukan Yaɗa Labarai na Tsaro, Maj.-Gen. Bernard Onyeuko, ya bayyana hakan a Abuja a wani taron manema labarai kan ayyukan sojojin tsakanin 28 ga Afrilu zuwa 19 ga Mayu.

“Tsakanin 1 – 14 ga Mayu 2022, jimillar ƴan ta’addar Boko Haram 1,627 da iyalansu sun miƙa wuya ga sojoji a wurare daban-daban.”

Ya ce dakarun Operation Haɗin kai sun kashe ƴan ta’adda 43, sun kama 20 tare da kuɓutar da mutane 63 da aka sace duk a yankin Arewa maso Gabas cikin makwanni uku.

Ya ce sojojin sun kashe wani kwamandan Boko Haram Abubakar Sarki a dajin Sambisa da ke Yuwe a karamar hukumar Konduga a jihar Borno, kamar yadda rahotannin baya suka tabbatar.

Ya ce sojojin, a wani samame na haɗin gwiwa da sojojin ƙasa da na sama suka yi a lokacin da suke gudanar da aikin share fage, sun kuma kashe babban hakimin yanƙin Gaita na Boko Haram, Malam Shehu da wasu daga cikin sojojin sa.

Ya ce sojojin sun kuma kama Mallam Modu Goni, wani ɗan ta’adda da ke sayar da kayayyaki a Kasuwar Bunin Yadi ga ƴan ta’adda bisa wani rahoto na hankali.

“A ci gaba da gudanar da ayyukanta, a ranar 17 ga Mayu, 2022, an kama Mallam Modu Pantami a wajen kauyen Benished a karamar hukumar Kaga a lokacin da yake ƙoƙarin jigilar kayayyaki masu yawa da ya saya domin kaiwa ga ƴan ta’adda a Gomari ƙauyen dake karamar hukumar Fere a jihar Borno.

“Sojoji sun gudanar da wani harin kwantan ɓauna a magamar ƴan ta’adda a ƙauyen Kaidieri, a sanadin harin aka kashe ƴan ta’adda biyar tare da kwato makamai iri-iri da alburusai daban-daban daga hannun ƴan ta’addan.”

Leave a Reply

%d bloggers like this: