Tsohon shugaban ƙasa, Olusegun Obasanjo ya bayyana cewa, Najeriya tana buƙatar shugaba ɗan gada-gada, wanda kuma yake da hauka, domin ya saisaita wa ƙasar zama tare da ɗora ta a saiti.

Obasanjo, ya bayyana hakan ne lokacin da ya karɓi baƙuncin ɗan takarar Shugabancin ƙasa, a karkashin jami’yyar PDP, Mohammed Hayatu-Deen, a gidan sa dake Abeokuta, a jihar Ogun.

Obasanjo yace, shi kansa wasu abubuwan da suka shafi Najeriya, sai da yayi su kamar a haukace, kuma baya neman afuwa akan hakan.

Yana da na sanin cewa, yanayin da ƙasar take ciki a yanzu haka, ba shi kaɗai yake sosawa rai ba, har ma da ƴan Najeriya waɗanda su ke buƙatar ganin Kyautatuwar kasar.

Tsohon shugaban ƙasar, ya kafe akan cewa Najeriya zata iya magance matsalar tsaro da take fuskanta a cikin shekara biyu kacal, idan aka sami nagartaccen shugaba, wanda yake a shirye domin ɗaukar kwakkwarar matsaya.

Daga nan kuma, sai Obasanjo yayi kira ga ƴan Najeriya da su tashi, su jajirce domin sadaukarwa wajen dawo da ƙasar kan turba.

Leave a Reply

%d bloggers like this: