Hukumar tsaro ta farin kaya, DSS, ta kama wasu ƴan Boko Haram guda biyu da ake zargi da tayar da bam a jihar Kano.

Hukumar DSS ta kwato wasu abubuwa masu fashewa daga hannun ƴan Boko Haram ɗin da aka kama.
Rahoton da muka samu ya bayyana cewa an kwato bindigogi kirar AK-47 guda huɗu, bindigu biyu, rigunan ƙunar baƙin wake, da wasu ababen fashewa da dama, daga hannun waɗanda ake zargin.

Cikin wani rahoto da Eons intelligence ya wallafa a shafinsa na Twitter ya ce:

“Bam-bam na KANO: Rahotanni sun nuna cewa bayan gudanar da aikin leken asiri, DSS ta kama wasu ƴan ta’addar #BH guda 2 kan harin bam da ya tashi a Kano.
Kayayyakin da aka kwato sun haɗa da bindigu ƙirar AK-47 guda 4, Bindigogi 2, Rigunan kashe-kashe da kayan haɗa IED da dama.
Wannan sabon ci gaba ya goyi bayan bayanan shaidun gani da ido cewa fashewar wani harin ƙunar baƙin wake ne.
Wannan na zuwa ne sa’o’i kaɗan bayan @elrufai @GovKaduna ya sanar da cewa # BH # ISWAP ta kwace ƙananan hukumomi biyu a jihar Kaduna.
Wannan nasarar da DSS ta yi, wataƙila ya ceci Kano daga babbar ranar kiyama.