Malamin makarantar jami’an da aka yi garkuwa da shi a makon da ya gabata Huzaifa Karfi ya shaki iskar yanci.

Huzaifa Karfi wanda ya ke koyarwa a jami’ar kimiya da fasaha ta Wudi dake Kano, an yi garkuwa da shi ne yayin da ya je kai kudin fansa ga yan bindigan da suka yi garkuwa da dagacin
Karfi a karamar hukamar Takai a Jihar Kano.

Sannan masu garkuwan dai_dai lokacin da suka saki mai sarautar gargajiy r sai suka rike Huzaifa a ranar Laraba.

A ranar Laraba data gabata ne wasu da ake zargi yan bindiga ne shiga kauyen Karfi inda aka hallaka mutane Shida tare da garkuwa da Dagacin Garin

Sai dai lokacin da muke hada wannan rahotan babu wata majiya da ta ce an biya kudin fansa

Leave a Reply

%d bloggers like this: